ZABEN RANAR 12 GA WATAN 1993 ABIOLA DA GWAMNATIN
MULKIN SOJA.
Daga: Abdullahi Musa Badayi.
Wannan rubutu zan yi shi ne sanadiyar roko dana nasu daga warin wasu matasa yan gwagwarmaya masu burin sanin hakikanin abubuwan da suka rafu akan wannan zabe.
Kuma rubutun zai kasance sadaukarwa ga Suleiman Yaro.
Wannan rubutun shima zai kasance mai dogon Zango ne zanyi kokarin yin bayani daki-daki yadda masu karatu zasu fahimta.
Wannan zabe na ranar 12 ga watan June ya kawo rudani musamman a fagen siyasar Najeriya, zabene da Gwamnatin mulkin soja ta Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ta soke shi. Duk da cewar ba'a bari hukumar zabe ta wachan lokacin NEC, wacce Farfesa Humpry Nwosu ke jagoranta ta gama fadin sakamakon zaben ba. Soke wannan zaben ya kawo kiyayya, gaba, da shakku a zuciyar yan Najeriya.
Soke zaben June 12 ya nuna karara yadda shugabanin siyasar Arewa, da manyan sojojin Arewa, da sarakunan Arewa, suka hada kai suka nuna cewar basu amince mulki ya koma kuduba. Hakan ya nuna yadda aka dannema Abiola hakkinshi da dokar kasar ta bashi.
Abiola ya lashe zaben fidda gwanine a birnin jos, ranar asabar 27 ga watan March 1993, wakilai 5, 215, suka kada kuru'unsu, Abiola ya lashe wannan zaben da kuru'u 272. Wanda wasu suke ganin Babu adalci tun anan wurin domin kuru'un da shi Abiolan ya lashe zabe dasu baza'a kirashi da gagarimin rinjayeba. Su kansu jam'iyun da Abiola da Bashir Tofa sukayi takara a cikinsu ba halatattutun jam'iyun siyasa bane dokokin soja ne suka kafa NRC, National Republican Convention, da SDP, Social Democratic party ranar 4 ga watan December 1989.
Bama jam'iyun kansu ba hattama shi dan Najeriya da zaije ya shiga jam''iya ba'a bashi zabiba, domin dukkanin jam'iyun guda biyu Gwamnatin mulkin soja ta Janar Babangida, ita ce ta zana jadawalunsu. Hakan ya sama jadawalin jam'iyun guda biyu babu wani banbanci. Ita kanta hukumar zaben Gwamnatin mulkin sojan ne ta kafata. Hattama ofishin jam'iyun na kasa, na jahohi, da kananan hukumoni Gwamnatin mulkin sojan duk ita ta ginasu akan kudi N 676.5m a jahohi 21 na Najeriya.
Itadai Gwamnatin mulkin sojan ta kashe N 546.6 m a wurin gina ofisoshi a kananan hukumomin Najeriya. Sauran kayanvaikin ofis Kuma na ofisoshin jam'iyun Gwamnatin ta mulkinvsoja ta siyosu a kudi N1.22 billoin, wanda a wanchan lokacin yazo dai dai da dalar amuruka $111.2 m.
A wata hira da akatabayi da Marigayi Abiola da Jaridar New Nigeria, a 1985, tun a lokacin Abiola yace idan da za'a bi shawararshi kada a kafa jam'iyu su wuce biyu. Abiola yace jam'iyu biyar da akayi a janhuriya ta biyu bata lokaci ne kawai da banar kudi.
ABIOLA YA LASHE ZABEN FIDDA GWANI.
Hakan ya samu asaline tun kusan shekarar 1991, bayan haramtama manyan yan siyasa da yawa sake tsayawa takarar shugaban kasa. Bayan manyan yan siyasan sun yi burus da wannan haramcin da Gwamnatin mulkin soja tai musu, sun Kuma ci gaba da harkokin siyasarsu. Gwamnatin mulkin sojan ta kamasu ta tsaresu ranar 2 ga watan December 1991, kuma aka kai su gaban wata hukuma wacce gwamnatin mulkin sojan ta kafa, wannan hukumar ta tabbatar da wannan haramcin akan wayannan manyan yan siyasan. Sune kamar haka Manjo Janar Shehu Musa Yar'adua rtd, Alhaji Lateef Jakande, Cif Bola Ige, Cif Solomon Lar, Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi, Cif Christain Onoh, Dr. Olusola Saraki, Cif Francis Authur Nzeribe, Alhaji Bello Maitama Yusuf Sardaunan Dutse, Alhaji Lamidi Adedibu, Mr. Paul Unongo, da Alhaji Lawal Kaita, haramcinnan ya sharema Abiola hanya.
Sharadin zaben fidda gwani a jam'iyar shi ne a samu sahihin zabe, kuma ya zamana wakilan da jam''iyar ta amince dasu ne sukayi zaben. Zaben da akayi ranar 16 ga watan October 1992 Marigayi Shehu Musa Yar'adua, shi ne ya lashe zaben a jam'iyar SDP, Alhaji Adamu Ciroma ya lashe a jam',iyar NCR.
Soke wanna zaben nasu Yar'adua ya biyo bayan matsin lambar daga kungiyar kiristoci ta Najeriya CAN tayi. Kungiyar CAN, tace duka jam'iyun biyu musulmai ne yan Arewa suka lashe zaben fidda gwanin, saboda haka dole a sokeshi. Olu Falae jigone a jam'iyar SDP, Kuma daya daga cikin wayanda Shehu Musa Yar'adua, ya kayarne a wata hira da yayi da wasu manyan yan jaridun Najeriya Tunji Olawumi, Kunle Oyatomi, Tina Ekemezie, da Deba Uwadiae, Falae ya Kira ga Gwamnatin mulkin soja tayi gaggawar soke wannan zaben. Falae yace bazai taba amincewa wasu mutane da baizabesu ba, su zama shugabaninshi.
Wasu daga cikin yan Jam'iyar, NRC sun rika yin kira da asokewannan zaben. Jaridar Abiola maisuna African Concord ta buga wani rahoto ranar 21 ga watan 1992 data samai sunan amubaranci da kudi, ta sake buga wani rahoton a mujallarta ta Concord ranar 12 ga watan October wanda taima sunan ba'a samu adalci ba, sam a zaben fidda gwanin da Yar'adua da Adamu Ciroma suka lashe, har ilayau Concord ta sake wallafa wani rahoton da taimai suna gwagwamaya tsakanin tsofaffin kayar yan siyasa.
Sannan sukace wai a karon farko zaben fidda gwani ya koma wurin yan Arewa, wayannan rahotannin mutane irinsu Peter Ishaka, Goddy Nnadi, Eniola Bello, Olusegun Adeniyi, Adeolu Durotoye da John Obozuwa suke rubutashi. Itama mujallar Newswatch tazo da irin nata salon kamar nuna wauta da kudi, an hana dimukuradiya walwala, ranar 5 ga watan October, ranar 7 ga watan December 1992 sunzo da wani rubutun da suka bashi taken karshen magudi.
A lokacin da jaridun kudu suke ganiyar yakar su Marigayi Shehu Musa Yar'adua, shima Abioal ba'a barshi a baya ba ya shigo cikin yakin gadan-gadan, idan yai Allah wadai da siyasar kudi, Abiola yayi wannan jawabin ga dalibai musulmai da suka kamnala jami'ar Obafemi Awolowo ranar litinin 21 ga watan September 1992.
Abiola yace babbar ilace yin amfani da kudi ka siyi kuru'un
mutane, duk gwamnatin da aka kafata da kudi zagaka batada cikakken goyan bayan jama'a. Ita kanta Jaridar Vanguard ta jawo hankalin mutane ta hanyar wani rubutu data sama suna kudawo cikin hankalinku. Duk yan takarkarun da suka ci zabe da kudi wanna ba halartaccen zabe bane, ya kamata Kuma su sani hakan bazai haifarma kasar da mai idoba.
A biyomu zamu dora gobe idan Allah ya bamu iko.