Comrade Abubakar Yahaya
An yi kira ga gwamnatin jihar Jigawa da ta kammala aikin sake gina hanyar mai tsawon kilomita daya a Harbo Sabuwa na karamar hukumar Jahun ta jihar.
Shugaban kungiyar ci gaban Harbo Sabuwa Alhaji shehu idris ne ya yi wannan kiran a wata hira da ya yi da gidan rediyon Najeriya a Dutse. Ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta kammala aikin yayin da damina ke gabatowa. Ya nuna godiyarsa ga gwamnatin jihar bisa sake gina rijiyoyin mai kilomita 20 daga Gunka zuwa Harbo Sabuwa.
Alhaji ShehuIdris yayi bayanin cewa aikin zai iya hana ambaliyarkowace shekara da Al’umma Harbo Sabuwa ke fuskanta. Ya bukaci gwamnatin jihar da ta gyara hanyoyin garin Harbo Sabuwa wadanda ke cikin mummunan hali sakamakon ambaliyar kowace shekara.
No comments:
Post a Comment